OPay da Palmpay Zasu Daina Aiki a Najeriya: CBN ta Bayyana Gaskiya

OPay da Palmpay Zasu Daina Aiki a Najeriya: CBN ta Bayyana Gaskiya

An rubuta wannan sakon ne don samar muku da bayani game da asalin rahoto da yake yaduwa cewa OPay da Palmpay Zasu Daina Aiki a Najeriya: CBN ta Bayyana Gaskiya, tare da cikakken bayani ko gaskiyane. 

Ga Maganan CBN

Babban bankin na kasa (CBN) ya mayar da martani kan wani rahoton da kafafen yada labarai suka fitar na cewa ya dakatar da ayyukan bankunan intanet guda 2, Opay da Palmpay.

OPAY da PALMPAY na daga cikin bankunan da babban bankin Najeriya ya baiwa lasisin gudanar da harkokin banki ta yanar gizo

Shugabannin kamfanonin 2 sun yi tsokaci kan labaran da ke yawo kan dakatar da ayyukansu a Najeriya.

A Abuja, Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta rahotannin da ke cewa ya dakatar da ayyukan bankunan yanar gizo na zamani, OPAY da PALMPAY, bayan gano cewa suna da hannu a damfara.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mukaddashin mai magana da yawun CBN, Isah Abdulmumin, ya ce labarin karya ne don haka ‘yan Najeriya su yi watsi da shi.

Daga ina Rahoton ya Fito?

A wata sanarwa da ta yi ta yawo a kafafen sada zumunta da ake dangantawa da Abdulmumin, ta yi ikirarin cewa CBN ta kammala shirin dakatar da ayyukan wasu cibiyoyin kudi guda biyu.

“Idan ba ka amfani da OPAY, PALMPAY ko wasu manhajojin su na Sinanci ko POS, to ka daina saka kudi da yawa a cikin asusun ko ka daina amfani da su.”

Sanarwan ya ce “CBN na gab da dakatar da ayyukan su saboda an gano cewa ana amfani da irin wadannan shirye-shirye wajen damfara.”

KU KARANTA: Yadda Ake Bude Asusun OPay da Duk Da Abeben da Yakamata ku Sani

Opay da Palmpay sun mayar da martani ga rahoton

Yayin da suke mayar da martani kan rahoton, OPAY da Palmpay, sun bayar da sanarwa tare da bayyana cewa suna gudanar da ayyukansu ne bisa ka’ida da ka’idojin CBN.

Opay ya bayyana cewa labarin da ke yawo cewa CBN zai dakatar da ayyukansa ba gaskiya ba ne kuma zai sauya ra’ayin mutane.

Hakazalika, Palmpay, ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan labari da aka kirkira domin a bata musu hankali.

OPAY da PALMPAY suna cikin kamfanonin hada-hadar kudi da ake kira Internet banking, wanda ke taimaka wa mutane wajen biyan kudi da sauran hada-hadar kudi.

KU KARANTA: Mafi kyawun Bankuna a Najeriya

Bankuna Suna Bi umarnin CBN na Zuwa Aiki A Karshen Mako

Sakamakon barazanar mamaye rassan CBN a jihohin Najeriya, babban bankin ya umarci bankunan kasuwanci da su fito a ranakun Asabar da Lahadi domin baiwa mutane kudi.

Zaku iya binmu a shafinmu na Facebook kan Zafin Labarai ko Twitter kan @Zafin_Labarai domin samun Wani talafi ko labarai da dumi-duminsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like